An kai hari a kasuwar Bagadaza | Labarai | DW | 28.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a kasuwar Bagadaza

Wani hari da wani dan kunar bakin wake ya kai ya halaka mutane 12 a wata kasuwar sayr da da kayan gwari da ke shake da jama'a, a dai dai lokacin da dakarun kasar ke fafatawa a yankin Tal Afar.

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Bagadaza, sun ce kasuwar da aka kai harin, galibin masu shiganta mabiya mazhabar Shi'a ne wadanda ke zaune, kuma maharin ya kutsa cikinta ne da mota shake da nakiyoyi. Ko da yake babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin, kungiyar IS dai ta kaddamar da hare-hare masu kama da shi a babban birnin na Iraki.

Harin na zuwa ne lokacin da hukumomin Irakin ke shirin bayyana samun nasarar kwato birnin Tal Afar, mai tazarar kilomita 400 da Bagadazan. Ma'aikatar cikin gida ta ce a daga cikin gawarwakin da aka samu, har da wasu 'yan sandan kasar su biyu.