1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Tunisiya na ci gaba da martani ga kafa sabuwar gwamnati

Mahmud Yaya Azare MNA
October 12, 2021

Al'ummar Tunisiya na ci gaba da mayar da martani ga kafa sabuwar gwamnati da aka yi a kasarsu, watanni uku bayan da Shugabar Kais Saeed ya karbe iko na gudanar da kusan dukkan harkokin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/41aLa
Tunesien Vereidigung neue Regierung
Hoto: Tunisian Presidency/REUTERS

Bayan da zanga-zangar adawa da matakin da ya dauka ta yi kamari a 'yan kwanakin nan, har wasu suka fara yin kira da yayi murabus, shugaban kasar Tunisiya Kais Saeed, wanda ya rantsar da Najla Bouden, mace ta farko a kasar a matsayin firaminista, ya ce yanzu yayi amannar cewa ya samu makamin yakin makiyan Tunisiya da ke ciki da wajen kasar.

"Daga cikin manyan kalubalen da za mu hada karfi da karfe don tunkararsu, ku 'yan kasa da kuma wannan sabuwar gwamnati, sh ine mu tabbatar da mun kwato kasarmu daga hanun kurayen da ke neman ganin bayanmu ciki da wajen kasarmu."

A jawabinta na farko bayan rantsuwar kama aiki, sabuwar Firaminista Najla Bouden, wacce ta lashi takobin inganta rayuwar al'ummar Tunisiya da maido da daraja da mutuncin gwamnatin kasar, ta kara da yin aiki haikan, don ganin bayan wadanda shugaban kasar ya siffanta su da miyagun kuraye da dodannin da ke shan jinin al'ummar Tunisiya.

Sabuwar firaministar kasar Tunisiya Najla Bouden Romdhane
Sabuwar firaministar kasar Tunisiya Najla Bouden RomdhaneHoto: Tunisian Presidency/REUTERS

"Yaki da cin hanci da rashawa da ke kara yin katutu a kullum a kasar nan shi ne babban dodon da ya zama wajibi da ko dai mu ga bayansa ku shi ya ga bayanmu. Domin mundin yana nan yana wanzuwa, babu ta yadda za'a ga wani ci-gaba na hakika ya tabbata a kasa."

A cikin sabuwar gwamnatin kasar ta Tunisiya akwai ministoci 25, tuni kuma 'yan kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan matakin da ya raba kan 'yan siyasar kasar biyu.

Karin bayani: Zanga-zangar adawa da shugaban Tunusiya

"Komi ya tsaya cik a kasar nan. Muna fata sabbin ministocin nan za su yi zuciya irinta shugaban kasa su sadaukar da kai don aiki tukuru na ceton kasarmu. Sata da wawason dukiyar kasa ya isa haka."

Babu alamun kawo karshen rikicin siyasar Tunisiya: Zanga-zangar adawa da Shugaba Kais Saeed
Babu alamun kawo karshen rikicin siyasar Tunisiya: Zanga-zangar adawa da Shugaba Kais Saeed Hoto: ZOUBEIR SOUISSI/REUTERS

Tuhamy Sa'adah na gamayyar kungiyoyin 'yan kwadagon kasar ya bayyana irin fatansa ga sabuwar gwamnatin.

"Abin da duk 'yan kasa ke jiran gani daga wannan sabuwar hukumar, ba a dinga bi ana kakkame mutane kan zargin sama da fadi da dukiyar kasa ba ce, wannan masifar tun bayan samun 'yanci ake yinta, ba za kuma a gamata ba, abin da ya fi damunmu shi ne inganta rayuwar jama'a da saukaka musu farashin kayayyakin masarufi da gyara tattalin arzikin kasa."

Ita kuwa babbar jam'iyyar adawa ta Ennahda cewa take "gwamnatin da ba ta samu halaccin amincewar majalisar dokoki ba, haramtacciyar gwamnati ce da ba za ta hidimta wa kasa ba.