1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

A karon farko mace ta zama firaministar Tunisiya

Suleiman Babayo AS
September 29, 2021

Shugaba Kais Saied na Tunisiya ya nada Najla Bouden Romdhane mace ta farko kan mukamun firaministar kasar.

https://p.dw.com/p/412hk
Tunesien | Najla Bouden Romdhane
Hoto: Tunisian Presidency/REUTERS

Shugaba Kais Saied na Tunisiya ya nada Najla Bouden Romdhane a matsayin mace ta farko kan mukamun firaministar kasar. Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ba da umurni ga sabuwar firaministar ta nada sabuwar majalisar ministoci cikin hanzari.

Ita dai sabuwar Firaminista Najla Bouden Romdhane tana da shekaru 63 da haihuwa, ta kasance farfesa tana koyarwa a daya daga cikin fitattun makarantun kasar. Wannan nadin na zuwa lokacin da kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin Afirka ke tsada da rikicin siyasa, bayan shugaban kasar ya rusa majalisar dokoki da kwace karfin iko ranar 25 ga watan Yuli na wannan shekara ta 2021.