1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil ta fito da sabuwar dokar mallakar bindiga

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 15, 2019

Sabon Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya sanya hannu a wannan Talata a kan wata ayar doka wacce za ta yi sassauci ga sharuddan samun lasisin izinin mallakar makamin bindiga a kasar. 

https://p.dw.com/p/3BbkI
Brasiliens Präsident Jair Bolsonaro unterzeichnet ein Dekret das den Waffenbesitz vereinacht
Hoto: Getty Images/AFP/E. Sa

Shugaba ya ce wannan mataki na a matsayin hanya mafi kyau wajen bai wa jama'a damar iya kare kansu da kuma rage kaifin matsalar tashe-tashen hankula da kasar ke fama da su. 

A karkashin sabuwar dokar lasin izinin mallakar bindiga wanda babbar hukumar 'yan sanda ta kasa ce ke ba da shi, zai yi aiki a wa'adin shekaru 10 a maimakon biyar a yanzu. Sai dai matakin zai shafi jihohin kasar da suka yi kaurin suna wajen kisan jama'a. 

Kazalika a karkashin dokar kowane dan kasar Brazil musamman mazauna yankunan karkara na da izinin mallakar bindigogi hudu kadai a maimakon shida a baya.