An kafa dokar hana fita a Adamawa | Labarai | DW | 30.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar hana fita a Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa a Najeriya, ta kafa dokar hana zirga-zirga a fadin jihar na tsawon makonni biyu, a kokarin da take yi na yaki da yaduwar cutar nan ta coronavirus.

Wata sanarwar da sakataren watsa labaran gwamna, Ahmadu Umaru Fintiri, wato Humwashi Wonosikou ya fitar, ta ce gwamnati ta Adamawa ta dauki matakin ne saboda kare rayukan al'uma daga barazanar da duniya ta shiga game da wannan annoba.

Dokar ta kuma shafi dukkanin ayyuka na masu kabu-kabu kama daga Keke Napep da motocin taxi da sauran na safa a fadin jihar, sai dai ta ya ware masu sayar da kayan abinci da magunguna da gidajen mai gami gami da bankuna, wadanda gwamnatin ta ce za su rika aiki amma a takaice.

Haka ma akwai matakin hana shige da fice tsakanin jihar ta Adamawa da sauran jihohin Najeriya da Jamhuriyar Kamaru, kuma duk za su fara aiki daga tsakar daren Talata.

Gwamna Umaru Fintiri, ya kuma ce wannan matakin ya zo ne bayan rashin bin wadda ta bukaci ma'aikata daga mataki na daya zuwa 14 da su zauna a gidajensu, saboda fargabar cutar.

Matakin ya zo bayan hana fita a jihohin Legas da Ogun da ma babban birnin Tarayya Abuja da Shugaba Buhari ya sanar da maraicen ranar Lahadi.