1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta binne gawar Soleimani

Abdul-raheem Hassan
January 7, 2020

Sama da mutane 30 sun mutu a hargitsi yayin jana'izar marigayi Janar Qassem Soleimani a mahaifarsa da ke Kerman, bayan da sojojin Amirka suka kashe shi a filin jirgin saman birnin Bagadaza na kasar Iraki.

https://p.dw.com/p/3VqJs
Iran Begräbnis von General Soleimani in Kerman
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Tasnim News Agency/E. Kouchari

Hukumomin kasar Iran ba su ayyana lokacin gudanar da binne gawar Soleimani ba ya zuwa yanzu, amma ana fargabar karuwar adadin wadanda suka mutu a turmutsitsi yayin jana'izar daga mutane 35.

A makon jiya ne dakarun Amirka suka kashe janar Qassem Soleimani a wani harin ta sama a filin jirgin saman Bagadaza babban birnin kasar Iraki. Harin da suka ce umarni ne daga Shugaba Donald Trump.

Tun dai bayan faruwar al'amarin ana ta hasashen zaman marina tsakanin Iran da Amirka bayan da Washington ta yi wa Teheran barazana idan ta dau fansa kan kisan.