An hallaka wani babban sojin kasar Burundi
August 2, 2015Talla
'Yan bindiga sun kashe daya daga cikin manyan habsoshin sojin kasar Burundi kana na hannun damar Shugaba Pierre Nkurunziza, lokacin da yake tafiya a cikin mota a birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar.
Jami'ai da shaidun gani da ido sun Janar Adolphe Nshimirimana babban jami'in leken asiri kuma wanda ake dauka mutum na biyu a gwamnatin kasar, ya gamu da ajalinsa lokacin da aka harfa rokoki guda biyu cikin motarsa inda nan take ta kama da wuta.
Lamarin na wannan Lahadi ya kara fitowa matsalolin da kasar ta Burundi take ciki tun lokacin da Shugaba Pierre Nkunrunziza ya yi tazarce bayan karewar wa'adin mulkinsa na shekaru 10. Tun lokacin ake nuna tsaron kasar za ta sake iya fadawa cikin yakin basasa.