An hallaka sojojin Saudiya a Yemen | Labarai | DW | 06.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka sojojin Saudiya a Yemen

Kasar Saudiya ta sanar da cewa an hallaka sojojinta 10 yayin wani hari da 'yan tawayen Houthi suka kai a rumbun adana makamai na sojojin kasar Yemen.

Rumbun adana makaman dai na nisan kimanin kilomita 120 da babban birnin kasar Sanaa wanda ke karkashin ikon 'yan tawayen na Houthi. Wannan dai ya kawo adadin sojojin rundunar taron dangin da ke ruwan bama-bamai a kasar ta Yemen karkashin jagorancin Saudiyan da suka rasa rayukansu a yakin na Yemen zuwa 55, bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da mutuwar sojojinta 45. Wannan dai shi ne karon farko da Saudiyan ta fito fili ta bayyana cewa sojojinta na fafatawa ta kasa a Yemen din tun bayan da ta shiga kasar a watan Maris din da ya gabata.