An hallaka daliban wata Jami′a a Amirka | Labarai | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka daliban wata Jami'a a Amirka

Wani matashi dan shekaru 26 da haihuwa, ya hallaka mutane 10 tare da jikkata wasu da dama a jami'ar Roseburg da ke cikin jihar Oregon a kasar Amirka

Wannan lamari dai ya janyo babban bacin ran shugaban na Amirka Barack Obama ganin yadda harbe-harbe a cikin makarantu a Amirka ya zamo ruwan dare gangama duniya. Wata daliba mai suna Cassandra Welding, da ke bada shaida ta gidan talbijin na CNN, ta ce tana cikin aji ne da ke kusa da ajin da mai harbin ya ke, lokacin da suka ji karan bindiga, sannan duk suka kwankwanta, amma kuma daya daga cikin abokanta da ta je lekawa, sai wannan harbi ya rutsa da ita.

Shugaban 'yan sandan yankin John Hanlin ya ce 'yan sanda sun bindige matashin mai suna Chris Harper Mercer bayan wani dan lokaci na harbe-harbe tsakaninsu kuma an samu bindigogi da dama a wurinsa. A kalla dai dalibai 3000 ne ke karatu cikin wannan jami'a, inda jami'an tsaro suka fitar da daliban tare da killace wurin.