1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Burkina masu yawa sun halaka

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 20, 2019

Sojojin gwamnatin Burkina Faso akalla 10 sun halaka a cikin wani gagarimin hari da wasu mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda suka kai wa ayarinsu tun da sanyin safiyar ranar Litinin a garin Koutougou na jihar Soum.

https://p.dw.com/p/3OB0X
Afrika Burkina Faso  l Militär
Hoto: DW/F. Muvunyi

A cikin wata sanarwa da rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta fitar inda ta bayyana harin a matsayin mafi muni da sojojin gwamnatin suka fuskanta a cikin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin, ta ce tana fargabar adadin sojojin da suka mutu a cikin harin na Soum da ke a arewacin kasar ya haura 20 ta la'akari da yadda ya zuwa yanzu ba a da duriyar da dama daga cikinsu. 

Sai dai rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta ce ta yi nasarar halaka da dama daga cikin maharan bayan da ta yi amfani da jiragen yaki da kuma kaddamar da wani farmaki ta kasa domin farautar maharan bayan aukuwar harin.