An gurfanar da waɗansu sojoji a Burundi | Labarai | DW | 17.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gurfanar da waɗansu sojoji a Burundi

Sojoji kusan 18 aka gurfanar a gaban kotu waɗanda ake zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura.

Hukumomi a ƙasar Burundi sun gurfanar da wasu mutane guda 18 yawancinsu sojoji, a gaban kotu sakamakon yunƙurin juyin mulkin da ya ci tura wanda suka yi wa shugaba Pierre Nkurumziza.

Kamfanin dilanci labarai na Faransa AFP ya ambato wasu na kusa da waɗanda aka cafken, suna shaida cewar, galibin waɗanda aka kama suna da raunika a jikinsu, har suka ce daya daga cikinsu ya kurumce a kune ɗaya, saboda mummunar dukkar da aka yi masa a gidan kurkun da ake tsare da shi.