An girmama ′yan sandan Faransa da ′yan ta′adda suka hallaka | Labarai | DW | 13.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An girmama 'yan sandan Faransa da 'yan ta'adda suka hallaka

Shugaba Faransa Francois Hollande ya shaida wa iyalan 'yan sanda uku da masu kaifin kishin Islama suka hallaka cewa jami'an tsaron sun mika rayuwarsu domin kare rayuwar al'ummar kasar.

Shugaba Hollande ya bayyana haka yayin girmama 'yan sandan uku da aka gudanar a wannan Talata, wadanda suka hada da Ahmed Merabet dan 40 kana Musulmi, da Franck Brinsolaro dan 49 da haihuwa, sai kuma Clarissa Jean-Philippe bakar fata 'yar shekaru 26.

A cikin wannan makon mujallar kasar ta Faransa mai zanen barkwanci ta sake dawowa bakin aiki bayan hare-haren da makon jiya da suka yi sandiyar halaka mutane 17. Mujallar ta Charlie Hebdo ta sake wallafa zaben na Annabi yana rike da wata takarda da ke nuna goyon bayan mujallar, kamar sauran mutanen duniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu