1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

An girka gwamnati a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

May 29, 2024

A hukumance an kaddamar da gwamnati a Kwango, bayan kwashe lokaci ana kwan gaba kwan baya a siyasar kasar bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watannin da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4gQEX
Hoto: TCHANDROU NITANGA/AFP via Getty Images

A wannan Labarar ne Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta gabatar da sabuwar gwamnati, abin da ya kawo karshen watanni biyar na takaddama bayan sake zaben Shugaba Felix Tshisekedi.

Daga dai cikin mukaman da gwamnatin ta bayyana, har da ministan tsaro da ta sanar da sunan Kabombo Muadiamvita.

Sanarwar bude sabon babin na gwamnati a Kwangon, na zuwa ne kasa da makonni biyu da sanarwar sojoji na murkushe wani yunkuri na kifar da gwamnati.

Sojojin sun yi ikirarin cewa wasu dauke da makamai sun tinkari gidan wani minista kafin daga bisani suka shiga fadar Shugaba Tshisekedi da ke a Kinshasa babban birnin kasar.