An gaza cimma matsaya a taron Yemen | Labarai | DW | 20.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza cimma matsaya a taron Yemen

A ranar Lahadin nan ce aka kammala taron sassantawa tsakanin wadanda suke takaddama da juna a Yemen ba tare da an cimma wata matsaya ba a bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Isma'l Ould Cheik Ahmed da ke zama manzon majalisar Dinkin Duniyar kan batun sulhun ya yi nuni da cewar bangarorin za su sake wani zaman a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2016.Kazalika Ya ce an tattauna muhimman batutuwa sossai ,to sai dai ba a kai ga cimma matsaya ba daga dukkanin bangarorin biyu na kasar.

Rikicin kasar ta Yemen dai wanda ya lakume rayuka sama da dubu 500 tare da tilastawa al'ummar kasar barin muhallansu masu tarin yawa ya janyo hankulan kasa da kasa ne ciki hadda kwamitin sulhu na MDD don warware rikicin.