1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cimma matsaya a Afirka ta Tsakiya

Abdul-raheem Hassan
November 15, 2018

Kasashen Rasha da Faransa da Amirka sun gaza cimma matsaya kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, gabannin wa'adin rundunar tabbatar kiyaye zaman lafiya na MDD.

https://p.dw.com/p/38HGN

A daren ranar Alhamis ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar amincewa da karin wa'adin ci gaba da zaman rundunar wanzar da zaman lafiya na MDD 12,000 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kasashen Rasha da Amirka sun kalubalanci yunkurin da kasar Faransa ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD da ke son ba wa sojojin wanzar da zaman lafiya damar horas da sojojin kasar.

Sama da dakaru 3,000 kungiyar Tarayyar Turai ta horas da aikin soji a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin da kasashen Rasha da Faransa suka ba da gudumuwar makamai da sauran kayan yaki da amincewar MDD.