An garkame wasu ′yan ta′adda a Senegal | Labarai | DW | 19.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An garkame wasu 'yan ta'adda a Senegal

An daure wasu mutame da suka yi yunkurin kafa wata kungiyar ta'addanci mai kama da ta Boko Haram a Senegal.

Gwamantin kasar Senegal ta daure wasu mutame 13 bayan samunsu da aka yi da yunkurin kafa wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da ke da kama da ta Boko Haram. Cikin watan Afirilun bana ne aka soma hukunta wasu mutane 30 saboda kasancewa cikin wannan yunkuri, bayan samun tabbacin wasun daga cikinsu sun ziyarci tungar Boko Haram da ke Najeriya.

Hukuncin da aka yanke wa mutanen, ya kama ne daga shekaru biyar zuwa shekaru 20, kuma jagoran kungiyar Matar Diokhan ne aka garkame shekrau 20. Kasar Senegal dai na bin matsakaicin tsarin dimukuradiyya ne, da kuma ke bin koyawar Islama da ke da sassauci.

A shekara ta 2015 ne kuma aka soma bincike kan jigon, bayan wallafa wani sakon jinjina wa wasu mayakan tarzoma da ya yi a shafin sada zumunta na facebook.