An gargadin Iran kan yarjejeniya da Amirka | Labarai | DW | 09.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargadin Iran kan yarjejeniya da Amirka

Sanatocin Amirka na jam'iyyar Republican sun shaidawa Iran cewa duk wata yarjejeniya da suka cimma da shugaba Barack Obama za ta dore ne kawai iya tsawon wa'adinsa.

A wata wasika da sanatoci 46 suka sanyawa hannu, sun ce dukannin wata matsaya da bangarorin biyu suka cimma kan shirin nukiliyar Iran za ta iya sauyawa in Obama ya bar iko a shekara ta 2017.

A cikin wasikar, 'yan majalisar dattawan na Republican suka ce shugaban da zai hau gadon mulki bayan Obama zai iya soke wannan yarjejeniya ba tare da bata lokaci ba kuma 'yan majalisar wakilai ka iya zama kanta don yi mata gyaran fuska.

Wannan wasika dai na zuwa ne bayan da a makon jiya firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu ya yi wani jawabi a zauren majalsiar dokokin Amirka din inda ya bukace da su tirjewa abinda ya kira kulla yarjejeniya da Iran wadda ba za ta haifar da da mai ido ba.