An gano kungiyoyin safarar mutane a Libiya | Labarai | DW | 08.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano kungiyoyin safarar mutane a Libiya

Matakin Majalisar Dinkin Duniyan ya bukaci toshe asusun bankin mutane da ke jagorantar kungiyoyin safarar bakin haure, tare da haramta musu tafiye-tafiye a kasashen ketere.

Wannan dai shi ne karo na farko da kwamitin sulhu na MDD ya fara daukar matakin ayyana takunkumi kan daidaikun kungiyoyi tare da takunkumi kan laifukan safarar jama'a.

Kasar Libiya ta yi kaurin suna wajen cinikin bakin haure bayan da kafar talabijin na CNN, ta wallafa bidiyon yadda ake gwanjon 'yan ci ranin Afirka a shekarar 2016.