An gano kayan kisan Khashoggi
November 13, 2018A kasar Turkiyya jaridar Sabah mai kusanci da gwamnatin kasar ta wallafa a wannan Talata hoton wani akwaiti mai kunshe da allurai da wasu kayan hida da na'urorin da ma wayoyin salula wadanda makasan dan jaridar nan na kasar Saudiyya marigayi Jamal Khashoggi suka yi amfani da su wajen aikata danyen aikin nasu a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul.
Wallafa wadannan hotuna na zuwa ne kwana daya bayan da jaridar New York Time ta Amirka ta wallafa wata murya da aka nada inda daya daga cikin makasan Khashoggi ke cewa wani mutun a kan waya, da ya sanar da mai gidansa cewa ya cika aikin. Ba a dai bayyana ba sunan kowane mai gidan ba a cikin muryar.
Amma jaridar ta New York Time ta ce jami'an leken asirin Amirka sun ce suna kyautata zaton mai gidan da mutuman ke magana ba kowa ba ne illa Yarima Mohammed Ben Salmane.