An gabatar da rahoton yakin Birtaniya a Iraki | Labarai | DW | 06.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gabatar da rahoton yakin Birtaniya a Iraki

Kwamitin bincike kan rawar da Birtaniya ta taka a yakin Iraki na shekara ta 2003 ya wallafa rahotonsa inda ya yi suka da kakkausan lafazi ga firaministan kasar na wancan lokaci wato Tony Blair.

Rahoton mai kunshe da kalmomi miliyan biyu da dubu dari shida, wanda kuma ya saurari shaidu 120 da suka hada da Tony Blair din da kansa, ya bayyana cewa an yaudari duniya da wannan yaki domin hujjojin da Birtaniyar da ma Amirka suka fake da su na kai wa Iraki yaki ba sahihai ba ne.

John Chilcot shugaban kwamitin wannan bincike da aka kafa yau shekaru bakwai da suka gabata ya ce Mr Blair ya sanar da cewa matakan sojan za su ba da dama a kawar da Kungiyar Al-Qaida da kuma kare kasar Birtaniya da kadarorinta, kana ya sanar da cewa mamayar Iraki za ta taimaka ga kwance mata damara ta tarin miyagun makaman da ta mallaka da ka iya karewa a hannun 'yan ta'adda, batun da ya tabbata ba gaskiya a cikinsa.

Sai dai da yake mayar da martani Tony Blair ya ce tsakanin shi da Allah ne ya dauki matakin shigar da kasar tasa a cikin yakin na Iraki, kuma a shirye yake ya amince da duk wasu kura-kuran da za a zarge shi da aikatawa a cikin yakin. Sojojin Birtaniya 179 suka rasa rayukansua cikin wannan yaki.