An fara zaben majalisun dokoki a Kamaru | Labarai | DW | 30.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara zaben majalisun dokoki a Kamaru

A wannan Litinin din ce aka bude rumfunan zabe domin gudanar da zabukan majalisun dokoki da na kananan hukumomi a Jamhuriyar Kamaru.

Schild am Gebäude der kamerunischen Wahlbehörde ELECAM (Elections Cameroon). Foto: DW/Dirke Köpp, Yaoundé, Kamerun, 09/10.09.2011

Wahlen in Kamerun kamerunische Wahlbehörde Schild ELECAM

Al'ummar Jamhuriyar Kamaru sun fara kwarara rumfunar zabe domin kada kuri'unsu a zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokoki karon farko tun shekara ta 2007.

Hukumar zaben kasar dai ta ce kimanin muntane miliyan biyar da kusan rabi ne za su kada kuri'un nasu a zaben wanda aka rigaya aka fara da misalin karfe takwas na safe agogon kasar kuma ana sa ran rufe rumfunan na zabe da misalin karfe shidda na yamma, agogon na Kamaru.

Tuni dai masu fashin bakin siyasa suka da sauran al'umma suka yi hasashen cewar jam'iyyar RDPC ta shugaba Paul Biya wanda ke kan madafun iko tun shekarar 1982 za ta samu gagarumin rinjaye a zaben.

To dai dai jam'iyyun adawa na kasar sun lashi takobin ganin ba a basu ruwa ba a zaben domin shiga majalisar kasar don a dama da su.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal