An fara tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 06.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara tsagaita wuta a Siriya

Rahotannin daga kasar Siriya na cewa bangarorin da ke yaki a kasar sun fara mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da kasashen Rasha da Iran da Turkiya suka cimma a birnin Astana na kasar Kazastan.

Fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Siriya da yaki ya dai-dai ta.

Fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Siriya da yaki ya dai-dai ta.

Kungiyar OSDH da ke sa ido a yakin na Siriya ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, tuni karar bindigogi ta lafa a biranen kasar da dama, tun baya ga wasu 'yan harbe harbe da karan tashin bama-bamai da aka ji a daren Jumma'ar da ta gabata da ma wayewar garin Asabar a jihar Hama da a tsakiyar birnin Damaskus da kuma arewacin birnin Alepo. Yarjejeniyar ta birnin Astana dai ta tanadi samar da tuddan natsira guda hudu a cikin jihohi takwas na kasar ta Siriya a tsawon wa'adin watanni 10.