An fara taron duniya kan sauyin yanayi
November 30, 2015Shugabannin kasashen duniya 150 sun hallara domin halartar taron ciki har da Shugaba Barack Obama na Amirka da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da na China Xi Jinping sai kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
A yayin taron na makonni biyu ana sa ran shugabannin kasashen duniya za su amince da rage dumamar yanyi zuwa digiri biyu a ma'aunin Celsius. Taron dai za a gudanar da shi cikin tsauraran matakan tsaro biyo bayan harin ta'addanci da birnin na Paris ya fuskanta makonni biyun da suka gabata inda mutane 130 suka hallaka.
Masu rajin kare muhalli dai na gudanar da zanga-zanga a fadin duniya dangane da zargin kasashen da kin daukar matakan da suka dace domin kare muhalli, inda a Berlin babban birnin kasar Jamus a kalla mutane 10,000 ke yin zanga-zangar.