An fara sauraron kalubalantar zaben shugaban Kenya | Labarai | DW | 27.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara sauraron kalubalantar zaben shugaban Kenya

A wannan Laraba kotun kolin kasar Kenya ke sauraron mahawara kan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar

A wannan Laraba kotun kolin kasar Kenya ke sauraron kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar, wanda Uhuru Kenyatta ya lashe cikin wannan wata na Maris, shari'ar da ke zama zakaran kwaji na demokaradiyyar kasar.

Firaminista Raila Odinga wanda ya zo na biyu, a zaben na ranar 4 ga wata ke kalubalantar sahihancin sakamakon zaben. Ranar Asabar wa'adin ke cika ga kotun na ta yanke hukunci kan matsayin sakamakon zaben shugaban kasar ta Kenya.

Rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa na shekara ta 2007, ya janyo mutuwan fiye da mutane 1200.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar