An fara samun sakamakon zaben Togo | Siyasa | DW | 27.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara samun sakamakon zaben Togo

Shugaba Faure Gnassingbe na kasar Togo ya kama hanyar sake lashe zaben da ya gudana a kasar da ke yankin yammacin Afirka

Hukumar zaben kasar Togo ta fara bayar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, bayan da ta tantance wani kaso na kuri'un da aka kada. Ya zuwa yanzu dai shugaba mai barin gado Faure Gnassingbe ne ke kan gaba da yawan kuri'i a kan abokan hammayarsa hudu.

Kashi 12 cikin 100 na kuri'un da aka kada hukumar zaben kasar Togo ta tantance ya zuwa yanzu. Sannan kuma runfunan zabe 934 na arewaci da Kudanci da kuma tsakiyar kasar ne kawai abin ya shafa, daga cikin runfunan kusan dubu tara da aka kada kuri'u. A kan wadannan alkaluma ne CENI ta dogara wajen bayyana shugaba mai barin gado Faure Gnassingbe a matsayin wanda yake kan gaba da yawan kuri'u inda ya lashe kashi 62 na kuri'un da aka kada. Madugun 'yan adawa Jean Pierre Fabre yana biye masa baya da kashi 32 na kuri'un da aka kada. Yayin da su sauran 'yan takara suka tashi da kasa da kashi daya daga cikin 100 na kuri'un da aka tattara.

Faure Gnassingbe wannan shi ne karo na uku da ya tsaya takara baya ga zabukan shekarun 2005 da kuma 2010 wadanda 'yan adawa suka kalubalanta. Sai dai kuma a wannan karon masu sa ido na kasa da kasa sun yaba yadda zaben shugaban kasar ya gudana a Togo. Andreas Jahn na daya daga cikin masu sa ido daga Jamus wanda ya nuna gamsuwa.

Ita dai Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Togo ta nunar da cewa kashi 53 zuwa 55 na wadanda suka yi rejista ne suka kadakuri'unsu: Lamarin da ya ja baya idan aka kwatanta da zaben shugaban kasa na 2010, inda kashi 64 na wadanda suka cancanta suka kada kuri'unsu. A cewar André Kangni Afanou da ke zama masanin siyasa, kana sakatare janar na gamayyar kungiyoyi fararen hula da ke yaki da cin hanci, wannan ba ya rasa nasaba da kin kwaskware dokokin zabe da hukumomi suka yi.

Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu na Togo sun bayyana cewa zaben na cike da kura-kurai. Amma masu sa ido na kasa da kasa sun nuna gamsuwa duk da wasu 'yan matsalolin da aka samu.

Duk dai da korafe-korafe da wasu 'yan Togo ke yi dangane da rashin gani a kasa, amma masu lura da al'amura na ganin cewa Faure Gnassingbe zai samu damar tazarce. Kusan shekaru 50 da suka gabata iyalan Gnassingbe ke gudanar da salon mulki gado a kasar da ke yankin yammacin Afirka, inda da ya gaji mahaifinsa duk kuma da ikarin bin tafarkin demokaradiya da wannan kasa ke yi. Nan da kwanaki masu zuwa ake sa ran samun cikekken sakamakon zaben.

Sauti da bidiyo akan labarin