An fara kwashe ′yan gudun hijira a sansanin Idomeni | Labarai | DW | 24.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kwashe 'yan gudun hijira a sansanin Idomeni

'Yan jarida dai an hana su danganawa da inda ake aikin kwashe 'yan gudun hijirar dan gani da ido yadda aikin kwashe su ke gudana.

Griechenland wildes Flüchtlingslager Idomeni

'Yan gudun hijira a Idomeni

Tun da sanyin safiyar Talatan nan ce mahukunta a kasar Girka suka fara aikin kwashe 'yan gudun hijira da ke zaune a sansanin Idomeni ba bisa ka'ida ba, a iyakar Macedonia inda suka rufe hanyar da za ta sada al'umma da wannan sansani bayan da aka sanya 'yan sandan kwantar da tarzoma sama da 400 kula da yankin.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Girka kan harkokin da suka shafi 'yan gudun hijira Giorgos Kyritsis, ya bayyana a ranar Litinin cewa 'yan sanda ba za su yi amfani da karfi ba wajen aikin kwashe 'yan gudun hijirar, aikin da zai dauki kwanaki bakwai zuwa goma ana gudanar da shi.

Wannan sansani dai na da 'yan gudun hijira 8,400 ne da ke san nausawa zuwa wasu kasashen Turai. A cewar mahukuntan na Girka da 'yan sanda za su kwashe su sannu a hankali zuwa wasu sansanoni da aka gina sabbi.