An fara bikin shekara na musamman na Kiristoci | Labarai | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara bikin shekara na musamman na Kiristoci

Bikin na lokaci zuwa lokaci yana zuwa yayin da ake samu tashe-tashen hankula a wasu yankunan da ake dangantawa da sabani na addini.

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bude bikin shekara na musamman da ake yi lokaci zuwa lokaci na shekara mai tsarki. Yayin da yake jawabi ga dubban mutanen da suka taru a fadar Vatikan yayin bude bikin ya nuna muhimmanci zaman tare musamman idan aka duba tashe-tashen hankula da ake samu.

An karfafa matakan tsaro da kimanin sojoji da 'yan sanda 5000 wadanda aka jibge a ciki da wajen birnin na Rome da ke kasar Italiya, yayin da ake sa ran masu ziyara na addinin fiye da milyan 10 za su kai ziyara zuwa shekara mai zuwa.