1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure wasu 'yan jam'iyyar adawa

Abdoulaye Mamane Amadou
August 9, 2019

Rahotanni daga yankin Douala sun ruwaito cewa daukacin wadanda aka yanke wa hukuncin 'yan jam'iyyar adawa MRC ne da ke goyon bayan jagoran 'yan adawar kasar Maurice Kamto.

https://p.dw.com/p/3NgBp
Kamerun Präsidentschaftswahlen Unterstützer von Maurice Kamto
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Kotun ta Kamaru daure wasu magoya bayan jam'iyyun adawa kimanin 40 har tsawon wa'adin watanni shida-shida a gidan yari, sakamakon kamasu da aikata laifin zanga-zangar nuna kyama ga sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoban shekarar bara, a yain da lauyan da ke kare jam'iyyar a yankin na Douala ya ce akwai yiwuwar daukaka kara idan har jam'iyyar adawar ta kammala cikakken nazari.