An daure wata ′yar Masar kan sukar Layya | Labarai | DW | 26.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daure wata 'yar Masar kan sukar Layya

An tisa keyar Fatima Naoot zuwa kotun masu aikata manyan laifuka a watan Disamba, bayan da lauyanta ya yi korafi, saboda batanci da ta yi kan ibadar Layya

Fatima Naoot

Fatima Naoot

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru uku ga wata mata marubuciya bayan yin rubutun batanci ga addinin Islama kamar yadda rahoton da gidan jaridar al-Ahram ya bayyana a shafinsa na intanet.

Marubuciyar Fatima Naoot har ila yau za ta biya tara ta fan din kasar Masar 20,000. Ita dai wannan marubuciya Naoot an sameta da laifin yin suka ga ibadar Layya da mabiya addinin Islama ke yi a duk shekara a lokutan babbar salla. Ta kuma yi wannan rubutun batanci ne a shafinta na Facebook.

An tisa keyar Naoot zuwa kotun masu aikata manyan laifuka a watan Disamba, bayan da lauyanta ya yi korafi. Sai dai taki amincewa cewa ta yi wa ibadar layyar batanci a nata ra'ayin dabbobin ne ke wahala a lokacin layyar.

A dai lokacin Eid al-Adha ko sallar layya miliyoyin mabiya addinin Islama da Allah ya huwacewa abin layya sukan yanka raguna shanu da rakuma da dai sauransu. Wannan marubuciya dai na da dama ta daukaka kara a kotun kolin kasar.