An daure wata mai raino a Yuganda | Labarai | DW | 15.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daure wata mai raino a Yuganda

Jolly Tumuhirwe 'yar shekaru 22 an kama ta da laifin cin zarafin karamar yarinya 'yar kasa da shekaru biyu, bayan da mahaifanta suka amince da ita don kula da 'yarsu.

Uganda Prozess Kindermädchen Jolly Tumuhiirwe

Jolly Tumuhirwe: Mai rainon da aka kama da cin zarafin karamar yarinya

Wani hoton bidiyo mai sosa rai da ya nuna wata mai raino a kasar Yuganda, tana duka tare da tattaka karamar yarinya da aka bata raino. Bayan wata shari'a a kasar ta Yuganda, daga wannan Litinin matar za ta fara zama a gidan kaso na tsawon shekaru hudu bayan da kotu ta same ta da laifi.

Jolly Tumuhirwe 'yar shekaru 22 an kama ta da wannan laifi bayan da mahaifin Arnella Kamanzi karamar yarinyar mai watanni 18 da haihuwa ya sanya wata na'urar nadar hoton bidiyo ta sirri a gidan nasa.

Hoton da mahaifin yarinyar ya nada ya gano matar tana duka da mari tare da tattaka yarinyar lokacin da take kuka.

Wannan hoton bidiyo da dubun daruruwan mutane suka gani bayan sanya shi a kafar sadarwar intanet da shafukan sada zumunta, ya sanya mahukunta a kasar ta Yuganda daukar matakan cewa duk wata mata da za a dauka aikin raino dole 'yan sanda su bincike ta kafin fara aiki.

Mahaifin yarinyar Eric Kamanz ya fada wa manema labarai cewa ko da yake ba su ma je ga abinda ya sami yarinyarsu ba, amma wannan hukunci zai zama darasi ga masu raino da ke da muguwar aniya.