1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin zama gidan yari ga Aung San Suu Kyi

Abdoulaye Mamane Amadou
September 29, 2022

An yanke wa tsohuwar shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa zarginta da cin amanar kasa

https://p.dw.com/p/4HUyU
Aung Suu Kyi shugabar Myanmar
Aung Suu Kyi shugabar Myanmar Hoto: Koen van Weel/picture alliance /ANP

Wata kotu a Myanmar ta yanke hukucin daurin gidan yari na tsawon shekaru uku ga tsohuwar shugabar gwamnati Aung San Suu Kyi bayan kamata da laifin cin amanar kasa ta hanyar taka dokar kare sirri.

Ko baya ga hambarariyar shugabar kotu ta kuma yanke hukuncin zama gidan kurkuku na tsawon shekaru uku ga tsohon mashawarcinta dan asalin kasar Australiya, masanin tattalin nan arziki Sean Turnell bisa tuhumarsa da taka doka.

Tun bayan da rundunar sojan kasar ta hambarar da ita kan madafan iko a shekarar 2021, rudanin  siyasa ya kara tsananta a kasar Myanmar tsakanin magoya bayan Suu Kyi da jami'an da suka karbe madafan iko.