1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakile yunkurin juyin mulki a Sao Tome

November 26, 2022

Hukumomi a Sao Tome, sun dakile wani yunkuri da aka yi na kifar da gwamnatin kasar. Yunkurin juyin mulkin da aka yi shi a ranar Juma'a, ya zo ne bayan rantsar da firaminista.

https://p.dw.com/p/4K7io
Patrice Trovoada
Hoto: DW

Jami'an tsaro a Sao Tome sun hallaka wasu mutane hudu tare da tsare wani fitaccen dan siyasar kasar Delfim Neves, bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Firaministan kasar, Patrice Trovoada ya ce mutanen da ake zargi da yunkurin na juyin mulki sun kutsa barikin soja a kokarinsu na kwashe makamai tare da yin garkuwa da wani jami'i.

Hukumomin kasar sun ce suna ci gaba da bincike kan ko wadanda suka aikata lafin sun samu wasu bayanai daga sojoji.

Firaministan ya kuma ce sun kore duk wani shakku kan ko mutanen sun yi kokari ne na aikata fashi ko kuma abu mai kama da hakan, domin bincike a matakin farko ya nunar da cewa kokari suka yi na kifar da gwamnati.

Lamarin dai ya zo ne watanni bayan zaben majalisar dokokin kasar da aka yi inda jam'iyyar Firaminsta Patrice Trovoada ta yi nasara.

A farkon wannan wata na Nuwamba ne dai aka rantsar da Firaminista Patrice Trovoada a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin kasar.