An dage zaben ′yan majalisa a Burundi | Labarai | DW | 20.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage zaben 'yan majalisa a Burundi

Shugaba Pierre Nkurinziza ya ce za'a matsar da zabukan 'yan majalisar da na kananan hukumomi daga ranar 26 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Yuni.

Wannan na zuwa ne a dandai lokacin arangama ta barke tsakanin masu gangamin adawa da jami'an 'yan sanda, a wannan kasa da ke da tsohon tarihin rikicin kabilanci da ya lashe rayukan dubban mutane.

Shugaba Pierre Nkurinziza ya ce za'a matsar da zabukan 'yan majalisar da na kananan hukumomi daga ranar 26 ga watan Mayu kamar yadda aka tsara a baya. Sai dai bai ambaci komai game da tashe tashen hankula daya dauki makonni yana gudana a fadar gwamnati ta Bujumbura ko kuma yunkurin kifar da mulki da baiyi nasara ba a makon da ya gabata.

Mai magana da yawun shugaban kasar ta Burundi ya fadawa manema labaru cewar, dage zaben nada nasaba da bukatun da jam'iyyun adawa suka gabatar da kuma kasashen ketare. Sai dai ba'a sauya ranar gudanar da zaben shugaban kasa ba kamar yadda aka tsayar a baya a ranar 26 ga watan Yuni.

Sai masana lamuran siyasa na ganin cewar, jinkirta zaben ba zai sauya komai dangane da adawa da takarar shugaba Nkurunziza a karo na uku ba, wanda suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar da ke bada wa'adi biyu ga kowane shugaba.