An daga kafa gwamnatin hadaka a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 07.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daga kafa gwamnatin hadaka a Sudan ta Kudu

Shuagban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun adawa Riek Machar sun tsawaita lokacin kafa gwamnatin gambiza daga 12 ga watan Nuwamba zuwa kwanaki 100.

Shugabannin biyu sun cimma wannan matsaya a makociyar kasar Uganda bayan wata tattaunawa. Dama bangarorin biyu da ke gaba da juna, sun amince da samar da gwamnatin hadaka a ranar 12 ga Nuwamba da zummar kawo karshen rikicin siyasar kasar tun bayan samun 'yancin kan kasar a 2011.

Tun 2013 kasar ke fama da rikicin siyasa wanda ya haddasa yakin basasa bayan rashin jituwa tsakanin Shugabannin, inda rikicin ya yi sanadiyar rayukan fararen hula da dama wasu miliyoyi kuma suka yi gudun hijira.