An cimma sabuwar yarjejeniya tsakanin Falasdinawa da Israila | Labarai | DW | 26.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma sabuwar yarjejeniya tsakanin Falasdinawa da Israila

Abin da ake saran zai kawo karshen makonni bakwai na yakin da ya yi sanadin mutuwar fiye da Falasdinawa 2,000.

Har yanzu dai babu wani tsokaci daga bangaren na Isra'ila kan amincewa da wannan yarjejeniya.

Ziad Nakhala, wani jami'i daga bangaren Islamic Jihad ya ce wannan yarjejeniya ba'a yi mata ka'ida ba zuwa wani kebabban lokaci, kuma Isra'ila za ta dage takunkumin rufe iyakarta ta yadda za'a samu damar shigar da kayan agaji zuwa Gaza da ma wasu kayan aikace-aikacen gini da ake bukata wajen sake gina wuraren da yaki ya daidaita.

Tattaunawa kan wasu batutuwa da suke da sarkakiya, kamar bukatar Hamas ta gina filin tashi da saukar jiragen sama da tashar jiragen ruwa wasu batutuwane da za'a sake koma wa kan teburin tattaunawa wata guda da ke tafe.

Nan gaba a ranar Talatannan ce Masar mai shiga tsakani za ta gudanar da jawabi kan wannan yarjejeniya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita:Abdurrahman Hassane