An ci zarafin mata a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 17.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ci zarafin mata a Sudan ta Kudu

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umarnin aiwatar da bincike kan matakin da dakarunsu suka dauka, yayin wani hari da aka kai a wani otel na birnin Juba.

Ban Ki-Moon ya nuna bacin ransa lokacin da aka gabatar masa da rahoto na karshe kan abubuwan da suka wakana a ranar 11 ga watan Yuli da ya gabata a wannan Otel, inda wasu mutane sanye da kayan soja suka kashe wani dan jarida, sannan suna yi wa mata da dama fyade a lokacin barkewar sabon fada tsakanin sojojin da ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da na mataimakinsa na wannan lokaci Riek Machar, inda ake zargin cewa dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, basu yi komai ba domin hana afkuwar lamari da ma wasu jerin cin zarafin mata da aka fuskanta a birnin na Juba.