An ci tarar shugaban Brazil na kin saka takunkumi | Labarai | DW | 13.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ci tarar shugaban Brazil na kin saka takunkumi

Hukumomin Brazil sun kama Shugaban Jair Bolsonaro da laifin karya dokar corona, zai biya dala 110 bayan da ya jagoranci dubban magoya bayan masu babura a titunan Sao Paulo ba tare da takunkumi ba.

Shugaban mai ra'ayin mazan jiya ya daga wa jama'a hannu a lokacin da yake kan babur din sa, sanye hular kwano amma ba takunkumi. Ko da yake Shugaba Bolsonaro ya gayawa mutane cewa takunkumin ba shi wani sauran tasiri ga wanda ya yi rigakafin corona, kalaman da ya haddasa kumfar baki daga masana kiwon lafiya a Brazil.

Zuwa yanzu ofishin shugaban kasar Brazil bai yi martani kan tarar da aka ci shugaban na take doka ba. Brazil na cikin kasashen duniya da annobar ta fi barnar kashe mutane baya ga kasashen Amirka da Indiya.