1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto wasu mutanen aKamaru

Abdourahamane Hassane
May 31, 2022

Sojoji a Kasar Kamaru sun kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su a yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4C67j
Nigerianischer Soldat auf der Halbinsel Bakassi
Hoto: AP

A ciki har da wata 'yar majalisar dattawa ta jam'iyyar shugaban kasar da aka yi garkuwa da su wata guda da ya gabata, a mafakar 'yan aware dake a Ashong a arewa maso yammacin kasar wato Elizabeth Regina Mundi tare da kashe wasu mutane 12 da ake zargi da yin garkuwa da su. Wadanda ake kyautata zaton cewar 'yan aware ne na Ambazonia. A ranar 30 ga watan Afrilu ne ‘yan tawayen da ke neman ‘yancin cin gashin kan yankin Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma suka yi garkuwa da Elizabeth.