1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano 'yan Thailand da suka bace a Kogo

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2018

Jami'an agaji sun tabbatar da samo matasa 'yan kwallon kafa 12 tare da mai horas da su a raye, bayan bacewar su cikin Kogo har tsawon kwanaki tara sakamakon ambaliyar ruwa.

https://p.dw.com/p/30hRf
Thailand Rettungsaktion in der Tham Luang Höhle
Hoto: picture-alliance/Xinhua

Masu ayyukan ceto sun ce dukkannin wadanda aka samu suna raye, kuma tuni aka tura jami'an kiwon lafiya domin duba lafiyarsu tare da tabbatar da basu dukkannin kulawar da suke bukata cikin gaggawa.

Hukumomin gwamnatin yankin da hatsarin ya faru a arewacin Thailand da ke makotaka da kasar Myanmar, sun bada tabbacin yashe ruwan da ke cikin Kogon domin samun damar ceto sauran mutane da kuma kauce wa fadawa irin hatsarin a nan gaba.