An cafke masu neman shiga Turai a Libiya | Labarai | DW | 11.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke masu neman shiga Turai a Libiya

Mahukuntan Libiya sun kama bakin hauren da ke neman tsallakawa da kananan jiragen ruwa ta barauniyar hanya zuwa nahiyar Turai domin inganta rayuwarsu.

Masu gadin gaban ruwan kasar Libiya sun cafke bakin-haure fiye da 400 cikin kwanaki biyu, masu neman zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya wajen amfani da kananan jiragen ruwa.

Jami'ai sun ce mafi yawan bakin-hauren sun fito daga kasashen Somaliya, da Eritrea, da Ghana, da kuma Najeriya. Wasu daga cikin mutanen an tsare su a ofishin 'yan sandan birnin Tripoli, inda jami'an kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka duba mutanen.

Matakin na kasar Libiya ya zo dai dai lokacin da mahukuntan kasar Italiya suka ceto kimanin bakin haure 4000 masu neman shiga Turai ta barauniyar hanya wajen amfani da kananan jiragen ruwa a farkon wannan wata na Afrilu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe