1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci shugaban Mali ya yi murabus

June 5, 2020

Dubban 'yan kasar Mali ne a wannan Juma'a suka yi dafifi a Bamako babban birnin kasar, inda suka yi ta kiraye-kirayen kawo karshen mulkin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

https://p.dw.com/p/3dKKr
Mali Amtsinhaber Keita Favorit bei Präsidentenstichwahl
Hoto: Reuters/L. Gnago

Boren na yau ya biyo makamantansa ne da aka yi ta yi cikin watan jiya, saboda bijire wa da sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da aka yi cikin watan Maris wanda ya bai wa jam'iyya mai ci nasara.

Haka ma galibin al'umar kasar ta Mali na fushi kan tsaurara dokoki da aka yi na yaki da annobar corona, a kasar da ke fama da hare-haren masu da'awar jihadi.

Yayin dai da wasu masu zanga-zangar ke kiran Shugaba Keita ya yi murabus, wasu kuwa kira suke da a sako tsohon Firaminista kuma jagoran hamayya, Soumaila Cisse, wanda aka yi garkuwa da shi ranar 25 ga watan Maris lokacin gangamin yakin neman zabe.