An kaddamar da shirin yaki da tsattsauran ra'ayi
May 16, 2019Talla
Shugabannin sun bayyana cewar shirin zai mayar da hankali ne wajen tace batutuwan da suka kunshi tunzura al'umma, da kuma cusa tsauraran akidun da suke haifar da rikici tsakanin al'umma, bincike dai ya tabbatar da yawan sakwonnin kai tsaye da jama'a suka dinga turawa juna a lokacin harin wasu masallatai a kasar New Zealand a watan Maris ya kai miliyan daya da rabi cikin kankanin lokaci.
A makon da ya gabata ne shugaba Macron na Faransa ya gana da Mark Zuckerberg shugaban kamfanin Facebook , don tattauna hanyoyin amfani da fasahar sadarwa ta hanyoyin da suka dace.