1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci EU ta tallafawa Kurdawan Iraki

August 11, 2014

Faransa ta bayyana cewa kamata ya yi kasashen Kungiyar Tarayyar Turai na EU su amsa kiran Kurdawan Iraki na ba su kayan yaki.

https://p.dw.com/p/1CsUR
Irak Laurent Fabius Pressekonferenz in Bagdad 10.08.2014
Hoto: AFP/Getty Images

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya fadi a ranar Litinin dinnan cewa kamata ya yi kasashen Kungiyar Tarayyar Turai na EU su amsa kiran Kurdawa 'yan Iraki na a tallafa wa mayakan su da kayan yaki dan tunkarar mayakan IS.

A cikin wata wasika da ya aike wa kantomar kula da harkokin wajen kungiyar ta EU Catherine Ashton, Fabius yace abune mai mahimmanci daga yanzu kasashen na turai su tashi dan bada wannan tallafi.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo