An bukaci dage zaben Burundi | Labarai | DW | 31.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci dage zaben Burundi

Shugabannin kasashen gabashin Afirka sun bukaci da a dage zaben Burundi da wata guda da rabi, kana sun nemi da a wanzar da zaman lafiya a kasar.

A wani taro da suka gudanar dazu a birnin Dar es Salam na kasar Tanzaniya, shugabannin gabashin Afirka suka ce sun damu da irin halin da ake ciki a kasar don haka shi ne ya sanya suka nemi dage zaben da kuma kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi.

Shugabannin dai sun so yin amfani da taron wajen neman shugaba Pierre Nkurunziza ya jingine neman tazarcen da ya ke da kuma sasanta shi da 'yan adawar kasarsa sai dai bai halarci taron ba, inda mai magana da yawunsa ya ce ba zai iya barin yakin neman zabensa ba don hallartar taron.

Kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa da sauran jama'ar gari dai na ta shirya zanga-zanga don nuna dawarsu da yin tazarce a kasar wadda suka ce ta sabawa kundin tsarin mulki sai dai Shugaba Nkurunziza ya yi watsi da bukatar al'ummar kasar kan wannan batu.