An bukaci Bahrain ta saki Nabeel Rajab | Labarai | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci Bahrain ta saki Nabeel Rajab

Kungiyar kare hakkin bani Adama ta Amnesty International ta bukaci mahukuntan Bahrain da su saki fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam na kasar Nabeel Rajab.

An dai tsare Nabeel ne tare da yi masa shari'a bayan da ya sanya wasu sakonni a shafinsa na Twitter wanda mahukuntan kasar suka ce cin zarafi ne gare su.

Amnesty din ta ce dukannin wani hukunci da za a yankewa Mr. Nabeel din zai kasance rashin adalci ne tsagwaronsa kuma hakan zai kara tabbatarwa da duniya irin yadda suke keta alfarmar bani Adama da dakile 'yancin fadin albarkacin baki. A farkon watan nan ne aka kama Nabeel Rajab wanda dan Shi'a ne bayan ya dau tsawon lokaci ya na sukar mahukuntan kasar.

Guda daga cikin irin sakonnin da ya sanya a Twitter a baya-bayan nan da ya harzuka mahukuntan kasar shi ne wanda ya ce wasu 'yan Bahrain din da suka shiga kungiyar nan ta IS 'yan Sunni ne da ke jibi da jami'an tsaron kasar. A Larabar nan da ke tafe dai ake sa ran yanke masa hukunci.