An bude tashoshin zabe a Baharain
November 24, 2018Talla
Manyan jam'iyyun adawa biyu Al-Wefaq ta 'yan Shi'a da Waad masu nesanta kai da addini an haramta masu shiga wannan zabe dalilin da ya jawo sabon kira na a kauce wa zaben 'yan majalisar a Baharain.
Sarki Hamad a watan Satumba ya nemi al'umma su fita zaben wanda jami'ai ke cewa akwai mutane 293 ciki har da mata 41 wadanda ke neman kujerun majalisa a kasar ta Baharain.
Da misalin karfe takwas agogon Baharain wato biyar agogon GMT aka bude tashoshin kada kuri'a yayin da za a rufe da karfe takwas na yamma.