1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron koli na kungiyar AU

February 17, 2024

Shugabannin kasashen Afirka sun fara taron koli na kwanaki biyu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a daidai lokacin da nahiyar ke fama da matsalolin mulki da tsaro da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4cVvw
Zauren taron koli na Kungiyar Tarayyar Afirka
Zauren taron koli na Kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: Solomon Muchie/DW

Shugabannin kasashen Afirka sun bude taron na 2024 a daidai lokacin da nahiyar ke fama da matsalolin juye-juyen mulki da tashe-tashen hankula da rikice-rikicen siyasa da ma na rashin tsaro da hauhawar farashin masarufi. An kuma gudanar da wani taron a rnar Juma'a a a gefen taron kolin na Kungiyar Tarayyar Afirka AU, domin samun hanyoyin sake wanzar da zaman lafiya a gabashin Jamhurinyar Dimokradiyar Kwango.

Kasashen Gabon da Nijar ba za su halarci taron ba sakamakon dakatar da su daga kungiyar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi. Kazalika hakan take ga kasashen Mali da Guinea da Sudan da kuma Burkina Faso. Ko baya ga matsalolin da nahiyar ke fuskanta, ana sa ran taron ya tattauna batun rikicin Zirin Gaza.