An bude taron kafafan yada labaru GMF da DW ke shirya a kowace shekara | Labarai | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kafafan yada labaru GMF da DW ke shirya a kowace shekara

Taron na bana na yini uku yana mayar da hankali kan sabbin fasahohin yada labaru na dijital da kuma tasirinsu a hulda tsakanin kasa da kasa.

Shugaban tashar DW Peter Limbourg ne ya bude babban taron kafafan yada labaru wato Global Media Forum da tashar ta DW ke shiryawa a kowace shekara a birnin Bonn. Taron na yini uku yana samun halartar 'yan jarida da shugabannin siyasa da na al'umma daga ko ina cikin duniya. Taron na bana na mayar da hankali ne kan irin tasirin da sabbin fasashohin yada labaru ke yi a dangantaka tsakanin kasa da kasa.

Mista Limbourg ke nan ya ce: "a duniya baki daya muna cin amfanin fa'aidar fasahar dijital musamman a fannin yada labaru da rahotanni da kuma hulda tsakanin jama'a."

Taron na bana ya zo daidai da bikin kaddamar da sabuwar tashar telebijin ta DW mai watsa shirye-shirye cikin harshen Ingilishi, inda za ta rinka bayar da labarai da rahotanni sa'o'i 24 ba kakkautawa. Tuni tashar ta saka wakilai a yankuna daban-daban na duniya don cimma wannan manufa.