An bude runfunan zaben raba gardama a Burtaniya | Labarai | DW | 23.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude runfunan zaben raba gardama a Burtaniya

A wannan Alhamis din ce 'yan kasar Burtaniya kusan miliyan 46 da dubu 500, za su kada kuri'unsu a zaben raba gardama kan ci gaba da kasancewar kasar a Tarayyar Turai.

Tun shekaru da dama ne masu adawa da kasancewar kasar ta Burtaniya cikin Tarayyar Turai ke ta nema da a yi wannan zaben raba gardama, wanda kuma a baya Firaministan kasar David Cameron ya sha alwashin gudanar da shi.

Wannan zabe dai zai taka babbar rawa kan makomar siyasar kasar ta Burtaniya, da ma ta Tarayyar Turai, wanda ake ganin idan har masu ra'ayin ficewa suka yi rinjaye, to kasar ta Burtaniya da Tarayyar Turai za su shafe tsawon shekaru wajen tattauna matakan wannan rabuwa mai cike da sarkakiya.