An buɗa taron Yamouscouro na Cote D´Ivoire | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗa taron Yamouscouro na Cote D´Ivoire

Bayan ƙiƙiƙaƙar da a ka fuskanta jiya, a ƙarshe dai, an buɗa taron birnin Yamouscouro na ƙasar Cote D`Ivoire, tsakanin ɓangarori daban daban masu gaba da juna, a wannan ƙasa.

Wannan taro, da shine irin sa na, farko tun ɓarkewar rikicin Cote D´Ivoire, a shekara ta 2002, ya samu halartar shugaban ƙasa Lauran Bagbo da madugun yan adawa Alassane Watara, da na yan tawaye, Guillaume Sorro, da kuma tsofan shugaban ƙasa, Henri Konan Bedie, sai kuma, praministan riƙon ƙwarya Charles Konnan Bany.

Wannan itace haɗuwar farko da aka yi, tsakanin shugaban ƙasa, da shugaban yan tawaye Guillaume Sorro, tun bayan ƙauracewar da yayi, daga gwamnatin haɗin kan ƙasa a shekara ta 2004.

A na gudanar da taron bisa cikkakun mattakan tsaro.

Shugabanin za su bitar halin da a ke ciki, a shirye shiryen zaɓen da a ke sa ran gudanarwa a watan oktober mai zuwa.

A na kyauttata zaton, su fido da sanarwar ƙarshen taro, a cikin daren yau.